Neymar ya buga wa Brazil wasa na 100

Neymar Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Alhamis tawagar kwallon kafa ta Brazil ta tashi 1-1 a wasan sada zumunta da ta yi da ta Senegal a Singapore.

A karawar ce Neymar ya yi wa Brazil wasa na 100, kuma tun kan fara karawar tsohon dan wasan Brazil, Bebeto ya bai wa Neymar rigar kasar Brazil mai dauke da lamba 100.

Bebeto ya buga wa tawagar Brazil wasa 75 ya kuma je gasar cin kofin duniya biyu a ciki ya lashe ta 1994 da aka yi a Amurka.

Kawo yanzu Neymar ya ci kwallo 61 a wasa 100 da ya yi wa Brazil, shi ne na uku a yawan cin kwallaye a tawagar, bayan Ronaldo da kuma Pele.

Neymar ya shiga jerin 'yan kwallon Brazil da suka buga mata wasa 100, bayan Cafu da ya yi 142 da Roberto Carlos mai 125 da Dani Alves da ya yi 116.

Sauran sun hada da Lucio da ya buga wa Brazil karawa 105 sai Claudio Taffarel da ya 101 da kuma Robinho da ya buga wasa 100.

Neymar ya ci lambar zinare a fagen tamaula a wasan Olympic da aka yi a Rio de Janeiro da aka yi a 2016.

Dan wasan ya yi rauni a karawa da Colombia a Quarter finals wanda hakan ya sa bai buga wasan da Jamus ta doke Brazil 7-1 a karawar kusa da karshe a kofin duniya da aka yi a 2014 ba.

Labarai masu alaka