An dakatar da dan wasan Liverpool

An dakatar da Harvey Elliott dan wasan gefen Liverpool daga buga duk wasu wasannin cikin gida na tsawon kwanaki 14, bayan samunshi da laifin cin zarafin Harry Kane a wani hoton bidiyo da ya fitar.

Dan wasan gefen ya shiga Liverpool ne a watan Yulin wannan shekarar, inda ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga gasar Firimiya a watan Mayu, ya fara buga wa Fulham wasa yana dan shekara 16 da kwana 30.

Wani bidiyo da Elliott ya sa a shafinsa na sada zumunta da muhawara, wanda kuma tuni ya roki gafara a kansa, ya janyo masa hukunci kan karya dokokin hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA.

Zai biya fam 350 a matsayin tara, ya kuma kara zama koyon wani kwas na sanin ilimin mu'amala da abokai.

Elliott mai shekara 16, ya sanya wani bidiyo ne da ya karya ka'ida a shafinsa na Snapchat yayin wasan karshe na gasar Zakarun Turai da Liverpool ta cinye Tottenham a watan Yuni.

Dan wasan ya ce an dauki bidiyon ne a gidan abokinsa, inda 7 daga cikin abokansa da ke goyon bayan Liverpool da na Tottenham suka rika fusata juna yayin wasan.

Liverpool na son tabbatar wa da hukumar FA cewa ba ta wasa da duk wani abu da ya shafi nuna wariya kuma ta ce ta yi wa Elliott magana lokacin da bidiyon ya fara karade intanet.

Tuni kyaftin din kungiyar Jordan Henderson ya yi masa bayani kan kalmomin da ke zama laifi idan aka yi amfani da su da kuma yadda mutane ke fahimtarsu.