Cristiano Ronaldo: Saura kiris ya bude sabon babi

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutum shida ne kacal suka taba zura kwallo 700

Saura kwallo daya Cristiano Ronaldo ya kai 700 a matsayin kwallayen da ya zura a raga bayan ya ci kwallo a wasan da Portugal ta lallasa Luxembourg da ci 3-0 a na cancantar shiga Kofin Turai na 2020.

Bernardo Silva na Manchester City ne ya fara cin bal kafin daga baya Ronaldo ya yi cafin ta saman mai tsaron raga Anthony Moris.

Dan wasan Valencia Goncalo Guedes ne ya rufe cin kwallayen ana gab da tashi daga wasan.

Portugal tana mataki na biyu a rukunin B, maki biyar a kasan Ukraine wacce ke saman teburi, maki hudu kuma a saman Serbia wacce take ta uku.

Ronaldo yana da damar zama daya daga cikin mutum shida kacal da suka taba zura kwallo 700 a raga a wasan da za su yi da Ukraine ranar Litinin.

Tawagar ta mai horarwa Fernando Santos za ta iya samun cancantar shiga gasar cin Kofin Turai ta 2020 ne kawai idan Serbia ta gaza cin Lithuania.

Labarai masu alaka