United ba za ta taya Harry Kane ba, Madrid na neman gola

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manyan kungiyoyi a Turai sun so sayen Harry Kane a baya

Mai horar da 'yan wasan Manchester United Ole Gunner Solskjaer, ya bayyana dan gaban Tottenham Harry Kane a matsayin daya daga cikin 'yan wasan da babu irin su a duniya, to amma ya ce zai yi wahala su iya rabo shi da kungiyarsa.

Manchester City na sa ido kan matashin dan wasan kulob din Napoli kuma dan kasar Spaniya Fabian Ruiz mai shekaru 23.

Ita kuwa Arsenal na shirin taya mai tsaron bayan kulob din Leipzig na Faransa Dayot Upamecano mai shekaru 20 da nufin kawo karshen baraka a bayanta.

A Italiya Juventus na kan tattaunawa da Mario Mandzukic kan yiwuwar barin kungiyar a watan Janairu mai zuwa.

Dama Manchester United na zawarcin dan wasan na Crotia mai shekaru 33.

A wani lamari mai kama da haka Manchester United na shirin kawo 'yan wasan gaba guda biyu a watan Janairu.

Akwai yiwuwar kulob din Monaco na Faransa ya taya dan wasan Aljeriya Islam Slimani da a yanzu yake zaman aro a kungiyar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Slimani dan wasan Leicester ne, sai dai ana ganin kulob din nasa zai bukaci a ba shi kudin da ya siyo dan wasan, fam miliyan 29 a shekarar 2016.

Real Madrid ta sanar da cewa za ta nemi mai tsaron gidan Athletic Bilbao Unai Simon mai shekaru 22, a matsayin wanda zai maye gurbin Thibault Courtois.

Mai horar da 'yan wasan Leicester Brendan Rodgers ya shawarci dan wasan tsakiyar kulob din James Maddison da ya tsaya ya ci gaba da shanawa a kungiyar.

Hakan ya biyo bayan rahotannin da ke cewa Manchester United ta nuna sha'awa kan sayen dan wasan.

Napoli na sa ran kulla yarjejeniya da Zlatan Ibrahimovic mai shekaru 38, bayan yarjejeniyarsa ta kare da kulob din LA Galaxy a watan Janairu.

Hukumar da ke shirya gasar firimiya ta Ingila na shirin gabatar da wani tsari da zai sa a kaucewa rudani a lokacin gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar.

Kakar wasan ta 2022 za ta fara kwanaki tara kafin fara gasar cin kofin, inda kuma za a dawo a ci gaba da gasar ta firimiya kwanaki takwas bayan an kammala wasan karshe na cin kofin duniya.