Champions League: Magoya bayan Liverpool sun yi batan kai

Lokacin da suka lura cewa sunyi batan hanyar zuwa Genk komai ya kure musu

Asalin hoton, Facebook.com/RADIO2005TVLAANDEREN

Bayanan hoto,

Lokaci ya riga ya kure masu lokacin da suka farga

Magoya bayan Liverpool biyu sun yi kuskuren zuwa Ghent domin halartar wasan da kungiyar ta fafata da Genk a gasar Zakarun Turai ta Champions League a daren ranar Laraba.

Rob, daga London da Lee daga Leicester, sun kashe kusan fan £200 wajen biyan kudin jirgin kasa da tikiti kawai, inda suka sauka Ghent tsawon Mil 95 kenan dga inda suka sauka zuwa inda Liverpool din ta buga wasan.

Rob ya shaida wa BBC cewa lokacin da suka isa wurin babu ko da mutum guda daga cikin magoya bayan kungiyar tasu ta Liverpool.

"Ko da muka ankare da hakan sai hankalinmu ya tashi," inji Rob.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sunan garin Ghentya yi kama da Kulob din Genk

"A lokacin muna cin abincin dare a wani wurin sayar da abinci, bayan kamar sa'a guda haka sai muka tambayi daya daga cikin ma'aikatan wurin wanda magoyin bayan Gent ne, za mu fafata da ku a daren nan sai kawai ya ce mana a'a.

"Hakan ta sanya muka lura da cewa shakka babu munyi batan hanya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gent ta gayyaci magoya bayan Liverpool din wasanta da Wolfsburg

"Mun kalli wasan a wata mashaya tare da dimbin mutane, kuma mun ji dadin kallon wasan, a cewar Rob".

Sai dai bayan jin matsalar da suka shiga ne, mazauna yankin suka gayyace su wasan da Gent din za ta yi da Wolfsburg a gasar Europa League a daren yau Alhamis.

Sai dai hakan ba zai yuwu ba, kasancewar ya kamata su koma Ingila a safiyar yau. Amma sun karbi tayin da aka yi masu na wasan da Gent din za ta yi da Genk a watan Janairu.

Rob ya kara da cewa: "Ina shakkun za mu sami damar sake zuwa garin amma muna iya komawa can a matsayin wadanda sunansu ya yi fice a yankin".

"Amma za mu samu wanda zai shirya mana tafiya idan irin hakan ta taso."