Champions League: Messi ya bude sabon babi

Lionel Messi

Asalin hoton, @FCBarcelona

Bayanan hoto,

Messi ya kamo Ronaldo da Raul da Ibrahimovic wajen zura wa kungiyoyi kwallaye a Champions League

Dan kasar Argentina din ya zura kwallon farko a gasar Zakarun Turai ta Champions League ta bana da yammacin ranar Laraba a wasan da Barça ta ci 2-1.

Cin kwallon da Mesi ya yi a wasan ya sanya sunan Slavia Prague cikin jerin kungiyoyin da ya zura wa kwallaye a gasar Champions League - 33 kenan jimulla.

Domin haka, Messi ya cimma tsohon dan wasan gaban Real Madrid da Schalke 04 Rául González da Cristiano Ronaldo da kuma Zlatan Ibrahimovic wajen yawan kwallayen da suka ci kungiyoyi daban-daban.

Kowannensu ya zura kwallo 29 a ragar kungiyoyi 33.

Kungiyoyin da Messi bai zura wa kwallo a raga ba su ne Rubin Kazan, Atlético Madrid, Benfica, Udinese, Levski Sofia, Borussia Dortmund da Inter Milan.

Dan wasan na da damar damar zura wa Borussia Dortmund da Inter Milan kwallo a sauran wasannin da suka rage na rukuni tun da da ma rukuninsu daya a gasar ta bana.

Tun daga 2005/2006 Messi ya ci kwallo a kakar wasa 15 ta Champions League a jere - dan wasa na farko kenan a Barcelona da ya taba yin hakan.