An zabi sabbin shugabannin hukumar kwallon kafar GFA ta Ghana

Mista Kurt Okereku sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Ghana wato Ghana Football Association (GFA)

Asalin hoton, @ghanafaofficial

Bayanan hoto,

Shekara hudu Kurt Okereku zai yi a jagorancin GFA

Hukumar kwallon kafa ta kasar Ghana wato Ghana Football Association (GFA) ta yi sabbin shugabanni bayan shekara da guda da rushe shugabannin nata bisa laifukan cin hanci da rashawa.

A jiya Juma'a ne dai aka gudanar da zaben, wanda Kurt Okereku ya lashe a matsayin shugaba bayan ya kayar da abokan hamayyarsa guda biyu.

A watan Yunin 2018 ne gwamnatin kasar ta rushe shugabancin hukumar bayan an ga shugabanta na lokacin Kwesi Nyantakyi a wani bidiyo na binciken kwakwaf yana karbar cin hanci daga dan jaridar da ya badda kama a matsayin mai zuba jari.

Dala $65,000 aka ce ya karba, kwatankwacin sama da naira miliyan 23. An kafa kwamitin rikon kwarya ne wanda ya ci gaba da jagorantar hukumar har zuwa lokacin zaben.

Mista Nyantakyi shi ne kuma mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Afirka wato CAF sannan kuma mamba a kwamitin Fifa wato Fifa Council.

An bude zaben ne da zaben mutum 120 a fadin kasar, wadanda za su rike mukamai daban-daban a GFA kafin zaben manyan 'yan kwamitin hukumar su 11.

Mista Kurt Okereku zai jagoranci hukumar na tsawon shekara hudu kafin a sake zabe a shekarar 2023.

Wannnan dai wani babban mataki ne na dawo da martabar kwallon kafa a kasar Ghana bayan waccan badakala da ta faru, musamman wasannin Firimiyar kasar.