Premier League: Tottenham ta sha kashi a hannun Liverpool

Christian Eriksen, Sadio Mane and Heung-Min Son

Asalin hoton, BBC Sport

Tottenham ta sha kashi a hannun Liverpool a wasaan Premier mako na 10 ranar Lahadi.

Yayin da Liverpool ta buga wasa 9 da aka buga kawo yanzu a kakar bana ba tare da ta yi rashin nasara ba, Tottenham na fuskantar akasin haka.

Kungiyar da ke birnin arewacin London ta yi rashin nasara sau 18 kenan a duka wasannin da ta buga bana.

Rashin tabuka rawar gani ya sanya aka fara rade-radin sallamar mai horar da yan wasan kungiyar, Mauricio Pochettino

Farkon wasan dai anyi tsammanin Tottenham din zata bada mamaki, la'akari da cewa itace ta fara zurawa Liverpool din kwallo a raga.

Kuma sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci kafin Liverpool ta farke, inda ta zura kwallo ta biyu a bugun finariti.

Tottenham dai ta zaburo a wasan zakarun turai a makon da ya gabata, inda ta casa kulob din Red Star Belgrade da ci 5-0.

To sai dai a daya bangaren, Liverpool na kan shanawa sosai fiye da kakar bara, kuma rabon da ta yi rashin nasara a filin wasanta na Anfield tun a watan Afrilun shekarar 2017, a lokacin da ta yi rashin nasara da ci 2-1 a karawarta da Crystal Palace.

Haka kuma canjaras daya kawai ta yi a wasanni 9 da aka buga kawo yanzu, a lokacin da ta ziyarci Manchester United mako biyu da suka wuce.

A bara kungiyoyin biyu sun tashi canjaras 2-2, a karawar da suka yi a filin na Anfield da ke birnin Liverpool.