Real Madrid za ta bayar da Bale ta karbo Pogba

Gareth Bale da kocin Madrid Zinadine Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid na son ba Manchester United fam miliyan £90 hadi da Gareth Bale, mai shekara 30, domin karbo Paul Pogba.

Sai dai ta bukaci dan wasan tsakiyar na Faransa ya tabbatar da yana kan ganiyarsa da nuna kwazo a fili. (El Desmarque, via Express)

Real Madrid kuma na son sayar da Bale da dan wasan Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, domin sayo dan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekara 20. (Calciomercato)

Shugaban Real Madrid Florentino Perez na shirin bin duk hanyoyin da suka dace domin karbo Mbappe zuwa Bernabeu a kasuwar musayar 'yan wasa mai zuwa. (AS)

Bayern Munich ta fara tunanin karbo dan wasan baya na Athletic Bilbao Unai Nunez mai shekara 20 wanda Arsenal da Everton suka nuna sha'awar suna so. (Goal.com)

Masu ba Arsenal shawara kan Mesut Ozil, mai shekara 31, sun son janyo ra'ayin dan wasan ya koma taka leda Amurka a gasar MLS. (Mail)

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce suna kan nazarin sayo dan wasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 21, wanda ya kulla yarjejeniya da Aston Villa a bazara. (Manchester Evening News)

Dan wasan Brazil Willian, mai shekara 31, ba ya son komawa kasarsa taka leda bayan kawo karshen yarjejeniyarsa a karshen kaka inda ya nuna sha'awar ci gaba da murza leda a Chelsea. (Metro)

Kocin Chelsea Frank Lampard yana fatan 'yan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 22, da Fikayo Tomori za su sabunta kwangilarsu a Stamford Bridge. (Goal.com))