Bundesliga: Lewandowski ya kafa tarihi a Bayern Munich

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lewandowski ya ci kwallo 19 a kakar bana

Robert Lewandowski ne dan wasa na farko da ya taba ci wa Bayern Munich kwallo a wasansa guda tara na farko a kakar wasa, inda Bayern din ta dare saman teburin Bundesliga bayan ta casa Union Berlin da ci 2-1.

Dan wasan gaban kasar Poland din ya ci kwallonsa ta 19 ne a kakar bana bayan an dawo daga hutun rabin lokaci bayan Benjamin Pavard ya ci ta farko.

Sebastian Polter ya farke wa Union Berlin guda daya amma Bayern ta rike wuta har aka tashi haka.

Ita kuwa Borussia Dortmund ta zama ta uku ne bayan ta tashi 0-0 a wasa tsakaninta da Schalke 04.

Nasarar ta bai wa Bayern damar darewa saman teburi da maki daya tsakaninta da Freiburg.

Borussia Monchengladbach da Wolfsburg za su iya dawowa mataki na biyu kowaccensu idan suka ci wasansu ranar Lahadi.

Lewandowski injin cin kwallo

Babu dan wasan da ya ci kwallaye ga kulob dinsa kamar Lewandowski a shekarar nan, inda ya ci 37 a 2019 - sama da Messi da Cristiano Ronaldo da Kylian Mbappe.

Kafin yanzu Pierre-Emerick Aubameyang ne ke rike da kambun, inda ya ci kwallo a wasa takwas na farkon kakar wasa ta 2015-2016 da ya buga a Dortmund.

Baki daya Lewandowski mai shekara 31 ya ci kwallo 37 a wasa 14 a dukkanin gasanni a kakar bana - a dukkanin wasa 13 na baya-bayan nan da Bayern ta buga.

Wasan da kawai bai ci kwallo ba shi ne wanda Dortmund ta cinye su da 2-0 a kofin German Super Cup da suka gwabza ranar 3 ga watan Agusta.

Har uku ya ci rigis a wasan da kasarsa Poland ta yi da Latvia na neman cancantar shiga kofin kasashen nahiyar Turai na Euro 2020, wanda suka buga a farkon watan nan.