Fifa U-17: Zan ci gaba da bin wasannin Najeriya sau da kafa - Buhari

Tawagar Golden Eaglets ta Najeriya

Asalin hoton, @thenff

Bayanan hoto,

Najeriya ce ta fi kowacce kasa daukar kofin gasar da kofinta biyar

Shugaba Muhammadu na Najeriya ya ce zai ci gaba da bin wasannin da kungiyar matasan Najeriya ta Golden Eaglets sau da kafa, wadda ke fafatawa a gasar cin Kofin Duniya ta 'yan kasa da shekara 17 da kasar Brazil ke karbar bakunci.

Shugaba Buhari yana bayyana jin dadinsa ne game da nasarar da matasan tawagar ta Golden Eaglets suka samu a wasan da suka ci kasar Hungary 4-2 a daren jiya Asabar.

"Wasanmu na farko a Brazil ya yi kyau matuka kuma ya sa ni alfahari," Buhari ya wallafa a Twitter.

Matasan Najeriya ne dai suka lallasa na kasar Hungary a wasan da aka zura kwallo har shida.

Kwallo shida rigis a wasan farko

Asalin hoton, @thenff

Bayanan hoto,

Najeriya aka fara ci a wasan

Gyorgy Komaromi na Hungary ne ya fara saka kasarsa a gaba minti 3 da take wasa kafin Samson Tijani ya farke wa Najeriya daga bugun finareti.

Hungary ta kara kwallo ta biyu ta kafar Samuel Major a minti na 28, inda shi kuma Usman Ibrahim ya farke ta a minti na 79.

A minti goman karshe na wasan ne matasan na Najeriya suka zura kwallo biyu ta kafar Oluwatimilehin Adenyi da kuma Samson Tijani.

Wannan nasara ta sa Shugaba Buhari ya ce da ma ya san za a rina: "Na tabbata sun shirya tsaf domin lashe kofin a karo na shida.

"Tun sanda suka sauka isa Brazil nake biye da su kuma na lura da irin himma da kwarin gwiwarsu. Wannan shi ne abin da aka san 'yan Najeriya da shi.

"Ni da kaina zan ci gaba da bibiyar wasanninsu a wannan gasar."

A tarihin gasar, Najeriya ce kasar da ta fi yin nasara inda ta lashe gasar har sau biyar a shekarun 1985 da 1985 da 1993 da 2007 da 2013 da kuma 2015 baya ga karewa a mataki na biyu da ta yi sau uku a gasar.

Najeriya dai tana rukuni na B tare da Hungary da Ecuador da Australia sannan za ta kara ne da Ecuador a wasa na gaba.

Matasan za su yi wasan karshe a matakin rukuni da Australia ranar 1 ga watan Nuwamba.