Klopp na son Kylian Mbappe, United na son Muller

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Ligverpool Jurgen Klopp na sha'awar sayo dan wasan gaban Paris St-Germain mai shekara 20, Kylian Mbappe. (Express)

Manchester City za ta sanya fan miliyan 100 kan dan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 22, a wani yunkuri na hana dan wasan komawa Bayern Munich.

Manchester United ta amince ta fitar da fan miliyan 125 domin sayo dan wasan tsakiyar Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 20, da dan wasan gaban Bayern Munich Thomas Muller, mai shekara 30. (Mirror)

Har wa yau, Manchester United ta janye sha'awarta kan dan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 30, saboda yawan jin rauni. (Mirror)

Bugu da kari Bayern Munich ba ta da madadin Muller, abin da zai hana dan wasan gaban nata damar tafiya a watan Janairu. (Goal.com)

Juventus da Napoli sun nuna sha'awa kan dan wasan gaban Tottenham da Korea ta Kudu Son Heung-min, mai shekara 27. (Express)

Real Madrid na kokarin dakushe fatan Arzenal yayin da take kokarin dawo da dan wasan tsakiyar Sifaniya Dani Ceballos, mai shekara 23, daga wasan aro da yake yi a kakar badi. (AS, via Mail)

Barcelona da Manchester United na sha'awar dan wasan Inter Milan Lautaro Martinez, mai shekara 22, amma dan wasan dan kasar Argentina an sanya farashin fan miliyan 96. (Sun)

Kazalika Barcelona ta tattauna da Inter Milan kan dan wasan tsakiyar Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 31. (Sport)

Manchester United da Manchester City na zawarcin dan wasan Rochdale dan kasar Ingila, Luke Matheson, mai shekara 17. (Star)

Napoli ba ta da sha'awar sayar da dan wasan tsakiyarta Fabian Ruiz a nan kusa, wanda Manchester City ke nema. (Gazzetta dello Sport, via Inside Futbol)

Inter Milan ta sanya Yuro miliyan 20 kan dan wasan Brazil Dalbert, mai shekara 26, wanda ya ta fi Fiorentina a matsayin aro. (Calciomercato)

Manchester City za ta sake bai wa dan gidan Wayne Rooney mai suna Kai, mai shekara tara, dama a karo na biyu a kwalejin horas da yan wasanta. (Star)