Man City na neman Fabian Ruiz, Juventus na neman Rakitic

A

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City na shirin zawarcin dan wasan tsakiyar Napoli Fabian Ruiz, mai shekara 23. (CalcioMercato)

Kocin Newcastle United Steve Bruce na shirin tayin aron dan wasan Chelsea mai shekaru 19 Reece James . (Sun)

Real Madrid na kokarin amfani da dangantakar da ke tsakanin dan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe da kocinsa Thomas Tuchel domin shawo kan dan kwallon Faransa mai shekaru 20. (AS)

Tsohon dan wasan tsakiyar Tottenham Hotspur da Netherlands Rafael van der Vaart ya ja hankalin Spurs din da ya sayi dan kwallon Morocco Hakim Ziyech, mai shekaru 26, daga kungiyar Ajax. (NOS)

Shugabannin Bayern Munich sun toshe damar dan wasan Jamus mai shekaru 30, Thomas Muller, wanda ake alakantawa da Manchester United, inda ake ganin zai bar Bayern a watan Janairu. (Mirror)

Asalin hoton, TF-Images

Dan wasan tsakiyar Croatia Ivan Rakitic, mai shekaru 31, na shirin sauya sheka a watan Janairu, yayin da United da Juventus suka sanya ido kan dan wasan. (Marca)

Southampton na son Erik Stoffelshaus, mai shekara 48 wanda ya yi aiki a Bundesliga wato Schalke da kulob din Rasha Lokomotiv Moscow, domin ya kasance sabon daraktan wasanni, inda Manchester United ita ma take da sha'awar kan sa. (Sun)

Wani mai daukar hoto na shirin aikawa da Brescia lissafin abin da ya kashe wajen gyaran kyamarar sa da ta lalace, bayan da tsohon dan wasan gaban Liverpool da Manchester City Mario Balotelli, mai shekaru 29, ya buge masa ita lokacin da yake cikin fushi, sakamakon sauya shi da aka yi a filin wasa. (Sun)