Salah da Liverpool na ci gaba da yi wa Spurs mamaya

Mohamed Salah scoring a penalty against Tottenham Hotspur

Tottenham dai ta fara kin jinin tattaki zuwa gidan Liverpool domin fafatawa a wasa, yayin da Mohamed Salah ake ganin zai fara jin cewa yana iya buga wasa da kungiyar a kowanne sati.

Zura kwallaye daga Salah da Jordan Henderson bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ya tabbatar wa Tottenham kwallon farko da ta zura a Anfield ranar Lahadi ba za ta dore ba.

Yanzu haka dai wasanni tara Kulob din ya yi da Liverpool ba tare da ya samun nasara ba, yayin da rashin nasara da ci 4-1 a Wembley cikin Oktobar 2017 shi ne kadai da Liverpool din ta yi a wasannin Premier 14 da suka gabata a hannun Tottenham.

Ganin yadda wasan ya wakana ranar Lahadi, ko da yake, watakila ba mamaki cewa 'yan wasan Pochettino ba su da kwarin gwiwar inganta yadda suke taka leda.

Yanzu haka dai wasan waje 11 ne Tottenham ba ta samu nasara a kansu ba. Wasa na karshe da Kulob din ya samu nasara a wasan aje shi ne wanda suka fafata da Fulham ranar 20 ga watan Janairu.

Hakan na nuni da cewa kungiyar za ta dauki tsawon lokaci tana jira kafin ta samu nasara a Premier.

Yanzu dai Liverpool ta ci nasara a wasannin guda 12 da suka wuce.