Pep Guardiola: 'Yan wasan Southampton kwararru ne'

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pep Guardiola

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Southampton wadanda su ka sha kashi da ci 9-0 a gida a hannun Leicester City ranar Juma'a "kwararrun 'yan wasa ne", in ji kocin Manchester City Pep Guardiola.

Kungiyar ta fafata a filin wasa na Etihad a gasar Carabao Cup ranar Talata ta kuma yi wasan Premier ranar Asabar, wasanninsu na farko tun bayan rashin nasara.

"Ba zan yanke hukunci a kansu ba ko kuma in shirya wasa tsakanina da su dangane da abin da ya faru da wasansu da Leicester ba," in ji Guardiola.

"Sun yi iya bakin kokarinsu."

'Yan wasan Southampton da kuma masu horar da kungiyar sun riga sun bayar da wani tallafi ga mabukata sakamakon nasarar mai tarihi da suka samu karon farko tun bayan shekara 134.

Duk da haka, ana tsammanin masu horaswar biyu zasu gudanar da sauye-sauye da dama, kuma Guardiola yana tsammanin kyakkyawar manufa.

Guardiola ya ce "ba abu ne mai sauki ba amma 'yan wasan kungiyar kwararru ne. Kocin su zai yi bakin ciki na wani lokaci amma bayan hakan dole ne za su ci gaba da kara kaimi.

"Mun san yadda kungiyar Leicester ta ke," Inji Guardiola .

"Amma gasa ce daban-daban, misali Kofin Carabao da Premier League. Kuma za mu yi kokarin mu kara shiri sosai don fuskantar kungiyoyi masu kyau."

A wani labarin kuma, kyaftin din Southampton Pierre-Emile Hojbjerg ya ce wasan ranar Talata wata dama ce ga 'yan wasan su da su kara zage dantse a filin wasan.