Granit Xhaka bai yi daidai ba – Unai Emery

Granit Xhaka takes off his Arsenal as he angrily walks off the pitch against Crystal Palace

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da magoya bayan Arsenal suka yi masa ihu a kakar bana

Kocin Arsenal Unai Emery ya ce Granit Xhaka ya yi "kuskure" lokacin da mayar da martani cikin fushi ga 'yan kallo bayan an sauya shi a wasan da kungiyarsa ta yi canjaras da Crystal Palace.

An rika yi wa kyaftin din Arsenal din ihu a lokacin da aka canja shi a filin wasa na Emirates bayan da ya tankawa masu yi masa ihun.

Daga nan ne kuma ya cire rigarsa, ya wuce ta gaban Emery kuma ya fita filin wasan.

"Dan wasan ya yi kuskure amma za mu tattauna game da batun," in ji Emery.

Ya ci gaba da cewa: "Ina so na natsu, amma gaskiya abin da ya yi bai kyauta ba."

A lokacin da aka sanar da sauya dan wasan an yi masa shewa ta ba'a, amma jin kadan ya sauya shi suka fara masa ihu yayin da yake tafiyar hawainiya kafin fita daga filin.

Ba wannan ne karon farko da magoya bayan Arsenal suka yi masa ihu a kakar bana ba, Emery ya fito fili ya kare dan kwallon wanda dan kasar Switzerland ne a wasansu da Aston Villa a watan jiya.