Ole Gunnar Solskjaer ya ce surutun mutane ba damuwarsa ba ne

Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Ole Gunnar Solskjaer ya ce duk da ya damu sosai da sakamakon wasannin Manchester United a kakar bana amma surutun da mutane ke yi game da shi ba damuwarsa ba ne.

Sai a gidan Norwich Manchester United ta samu nasara a wasannin da take kai ziyara inda ta doke ta 3-1.

Solskjaer na fuskantar kalubale da barazanar kora saboda yadda Manchester ta fara kaka da kafar hagu.

Solskjae ya shaida wa BBC cewa "Wadanda ya kamata su aminta da ni da kuma wadanda ke da muhimmanci, ba su damu ba,"

Tazarar maki biyu kacal ya raba Manchester United da kasan teburin Premier inda ta ke matsayi na 15 kafin wasanta da Norwich.

Amma maki ukun da ta samu a gidan Norwich ya ba ta damar haurowa matsayi na bakwai.

Wasan shi ne karo na biyu da Manchester United ta ci fiye da kwallaye biyu a wasa tun bayan doke Chelsea 4-0 a ranar farko da aka soma Premier.

Solskjaer ya ce ya damu da sakamakon wasannin United.

"Ban damu da surutun mutane ba, kowa yana da ra'ayinsa kuma ba damuwa ta ba ne na yi tsokaci kan kalaman wasu, ban damu da abin da wani zai ce game da ni ba.