Gareth Bale ya roki Real Madrid, Shanghai Shenhua na neman Bale

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 30, ya roki Real Madrid kada ta wallafa bayanan da suka shafi lafiyarsa, kamar yadda dokar Spain ta ba shi dama. (ESPN)

Shanghai Shenhua ta sake nuna sha'awar karbo Gareth Bale. (Marca)

Bale ya tafi London domin ganawa da wakilinsa a ranar Litinin yayin da yake fuskantar tabbas kan makomarsa a Real Madrid . (Mail)

Real Madrid ta ce tsohon dan wasan na Tottenham ya ta fi London ne domin wasu harakokinsa. (Marca)

Manchester United ta nuna sha'awar karbo 'yan wasan Faransa biyu Boubakary Soumare, mai shekara 20 daga Lille, da kuma dan wasan LyonMoussa Dembele, mai shekara 23. (ESPN)

Kaftin din Arsenal Granit Xhaka, mai shekara 27, ya karbi bakuncin wasu tsoffin 'yan wasan kungiyar da suka kai masa ziyara saboda boren da ya yi sakamakon fitar da shi wasa a ranar Lahadi da Arsenal ta yi canjaras da Crystal Palace. (The Athletic)

Arsenal za ta gana da Xhaka na 'yan kwanaki domin tattauna al'amarin. (Sky Sports)

Alexandre Lacazette na Arsenal ya goyi bayan kalaman da Xhaka ya wallafa a Instagram inda yake kira da a kori kocinsu Unai Emery. (London Evening Standard)

Ana sa ran dan wasan baya na Ingila Chris Smalling, mai shekara 29, zai dawo taka leda Manchester United daga Romainda ya tafi a matayin dan wasan aro duk da rade-radin zai ci gaba da taka leda a kungiyar ta Italiya. (Sky Sports)

Dan wasan tsakiya na Liverpool James Milner mai shekara 33, yana son ci gaba da zama a kungiyar fiye da kwangilarsa za ta kawo karshe a karshen kakar bana. (Guardian)