An dakatar da Frank Ribery wasa uku

Franck Ribery

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Franck Ribery (daga hagu) ya ci kwallo biyu a wasanni tara da ya yi bayan komawa Fiorentina

An dakatar da dan wasan kungiyar Fiorentina Frank Ribery daga buga wasa uku, tare da cin sa tarar Yuro 20,000 (fan 17,257) bayan ya ture mataimakin alkalin wasa, a wasan da Lazio ta doke su da ci 2-1.

Dan kwallon, mai shekara 36, wanda aka cauya shi a minti na 74, ya kalubalanci mataimakin alkalin wasa a lokacin da aka tashi wasa.

Daga nan ne sai aka ba shi jan kati.

Ribery, wanda ya koma wata kungiyar da ke wasa a gasar Serie A a kakar bana, ya nuna nadamarsa.

Wani kwamitin ladaftarwa na gasar Serie A ya bayyana abin da Ribery ya yi da "babban rashin ladabi" inda ya ce dan wasan ya tunkari jami'in wasan yana masa "barazana" kuma ya ture shi har sau biyu.

Bayan faruwar lamarin, tsohon dan wasan Bayern Munich ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: Ina neman afuwa daga takwarorina 'yan wasa da kocinmu da kuma magoya bayanmu."

"Hakazalika ina neman gafarar mataimakin alkalin wasa Mista Passeri saboda raina ya baci a karshen wasan kuma ina fatan zai fahimci hakan."

Kungiyar Fiorentina ta yi ikirarin cewa abin da ya faru ne ya ba Lazio damar samun nasara a kanta, inda dan wasa Ciro Immobile ya zura mata kwallo ta biyu a raga.