Unai Emery: 'Ya dace Xhaka ya nemi afuwa'

Granit Xhaka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

"Gaskiya ne, Xhaka ya san ya yi kuskure kuma ya damu sosai," in ji Emery

Kocin Arsenal Unai Emery ya ce ya kamata Granit Xhaka ya nemi afuwa bayan ya mayar wa magoya bayan kungiyarsu martani a wasan da suka buga canjaras 2-2 da Crystal Palace.

An rika yi wa kyaftin din Arsenal din ihu a lokacin da aka sauya shi a filin wasa na Emirates.

Daga nan ne kuma ya cire rigarsa, ya wuce ta gaban Emery kuma ya fita filin wasan.

Emery ya ce: "Eh ya kamata ya nemi gafara. Mun yi kuskure, ya kamata mu nemi gafara kuma mun ba shi shawara ya yi hakan.

"Gaskiya ne, ya san ya yi kuskure kuma ya damu sosai."

Ba wannan ne karon farko da magoya bayan Arsenal suka yi masa ihu a kakar bana ba, Emery ya fito fili ya kare dan kwallon wanda dan kasar Switzerland ne a wasansu da Aston Villa a watan jiya.

"Dan kwallon ya yi atisaye da sauran 'yan wasa, kuma ya damu matuka da abin da ya faru," in ji kocin.

Xhaka ba ya cikin 'yan wasan Arsenal da za su fafata da Liverpool a ranar Laraba, sai dai Emery ya ce dama zai rika sauye-sauye a kungiyar.

Sai dai kocin bai bayar da tabbacin cewa Xhaka zai ci gaba da zama kyaftin din kungiyar ba.