Bulgaria za ta yi wasa biyu ba tare da 'yan kallo ba – UEFA

'Yan wasan Ingila lokcin d magoya bayan Bulgaria ke yi musu ihu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Ingila lokacin da magoya bayan Bulgaria ke yi musu ihu

An umarci Bulgaria ta buga wasanni biyu ba tare da 'yan kallo ba saboda kalaman nuna wariyar da magoya bayan kwallon kafar kasar suka yi wa 'yan wasan Ingila a wasan neman shiga gasar Euro 2020 a a birnin Sofia.

Sau biyu ana dakatar da wasan da Ingila ta samu nasara da ci 6-0, sai dai hakan bai hana karasa wasan ba.

An rufe filin wasan da tun farko aka shirya yin fafatawar sakamakon matsalar nuna wariya.

Hakazalika hukumar UEFA ta ci tarar Bulgaria kudi kimanin Yuro 75,000.

Magoya bayan Bulgarian dai sun yi ta furta kalaman nuna wariya da suka hada da alamomin 'yan Nazi da kuma kukan biri.

Hukuncin da aka yi wa Bulgaria na nufin za su buga wasansu na karshe na neman tikitin shiga gasar Euro 2020 ranar 17 ga Nuwamba ba tare da 'yan kallo ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Filin wasan Bulgaria

Hukumar yaki da nuna wariya ta ce "abin takaici ne" ba a dakatar da Bulgaria daga wasan neman shiga gasar cin kofin Euro 2020 ba" saboda abin da suka yi a baya da kuma gazawa wajen magance matsalolin nuna wariyar launin fata".

Hukumar ta ce "akwai hujjojin da suka nuna cewa akwai bukatar daukar matakan dakile matsalkar nuna wariya, musamman yadda ya fito karara a bangaren kwallon kafa".

"Za mu ci gaba da bibiyar UEFA don tabbatar da cewa Bulgaria da sauransu da ke fama da wannan matsalar sun yi dukkan mai yiwuwa don magance matsalolin nuna wariyar launin fata."

An ci tarar Ingila Yuro 5,000 bayan da magoya bayansu suka yi ihu a lokacin da ake taken Bulgaria kafin wasa, yayin da aka ci tarar wadanda suka karbi bakuncin wasan Yuro 10,000 sakamakon laifin da magoya bayansu suka yi.