Batanci: An dakatar da Francesco Magnanelli da Matteo Scozzarella

'Yan wasan da aka datakar sakamakon aikata sabo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan da aka datakar sakamakon aikata sabo

An dakatar da wasu 'yan wasan Italiya wasa daya sakamakon samun su da laifin sabo lokacin da suke fafatawa a gasar Seria A.

An nuno dan wasan Sassuolo Francesco Magnanelli da kuma dan wasan Parma Matteo Scozzarella a talabijin suna furta kalaman sabo a wurare daban-daban.

Akwai tsauraran matakai kan duk wanda aka samu yana shagube da sunan Allah a Italiya.

Ko a shekarar 2010 ma hukumar kwallon kafar kasar ta ladabtar da 'yan wasan da aka samu da aikata laifin.

A shekarar 2018 an dakatar da dan wasan tsakiyar Udinese Rolando Mandragora, sakamakon aikata makamancin laifin.