Alkalan wasa za su gana kan batun na'urar VAR

Alkalin wasa lokacin da ya ke duba na'urar VAR

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalin wasa lokacin da ya ke duba na'urar VAR

Alkalan Premier za su gana a makon nan kan batun yadda ake amfani da na'urar taimaka wa alkalan wasanni a fili.

Wannan na zuwa ne bayan da aka fuskancin sarkakiya a hukuncin da aka yanke yayin wasannin da suka gudana a karshen makon jiya.

Ganawar da kwararrun alkalan wasanni zasu yi, na zuwa ne bayan da na'urar ta VAR ta bayar da bugun finariti hudu da jan kati da kuma soke kwallon da aka zura a ragar a manyan wasannin karshen makon da ya gabata.

Kafin haka, na'urar VAR ba ta bayar da bugun finariti ko jan kati ba, a wasanni 90 da aka fafata.

An kuma soki lamirin rashin amfani da majigin filin kwallon da alkalan wasanni suka gaza yi.

"Ita ce kadai gasa a duniya inda aka gaza karfafawa alkalan wasanni gwiwa da su sanya idanu a kan wasa sosai.

"Abin kunya ne," tsohon dan wasan tsakiya na Wales Robbie Savage da ya shaida wa BBC.

Manufar majigi a filin wasa ita ce amfani da su wajen kare martabar kwallon kafa a Premier.

Yawancin lokaci ana amfani da su ne lokacin da alakalin wasa hankalinsa bai kai wurin da aka samu matsala ba, ko kuma abin da aka shaida wa jami'in wasa bai yi dai-dai da abinda ya gani ba.

Manyan kungiyoyin na iya tattaunawa kan batun yayin da suka gudanar da daya daga cikin taronsu na yau da kullun a ranar 14 ga Nuwamba.

Taron da za a gudanar ya kunshi wasu daga cikin mambobin kungiyoyin alkalan wasanni da mataimakansu, wadnda kan hallara sau biyu a wata don yin nazari kan yadda za a inganta wasanni, horo da kuma fasaha.