Man City za ta kara da Oxford United a Carabao Cup

Colchester United ta kai zagayen gab da na kusada karshe a gasar karon farko bayan da ta doke Crawley Town

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Colchester United ta kai zagayen gab da na kusa da karshe a gasar karon farko bayan da ta doke Crawley Town

Mai rike da kambun gasar, Manchester City, za ta yi wasanta na dab da na karshe a gasar cin kofin Carabao da Oxford United.

Zagaye na biyu kuma Colchester United, wadda ke karshe-karshe a rukuni za ta fafata ne da Man United wadda ta taba lashe gasar har sau biyar a baya.

Liverpool wadda ta taba lashe gasar har sau takwas a baya, za ta yi tattaki zuwa gidan Aston Villa, yayin da Everton za ta kara da Leicester City.

Wasanni tsakanin kungiyoyin an shirya gudanarwa ne a watan Disamba, inda za a fara ranar Litinin 16 ga wata.

Akwai yiwuwar a sauya ranar da Liverpool za ta yi wasanta da Aston Villa, yayin da take shirye-shiryen fafatawa a gasar FIFA ta Kulob-Kulob da za a yi ranar 18 ga watan Disamba.

Hukumar shirya gasar Carabao Cup din dai tana tattaunawa da Liverpool don tantance ranar da za Liverpool za ta buga wasanta na cin kofin duniya na kungiyoyin kasashe," in ji kakakin hukumar.

Liverpool ta doke Arsenal 5-4 a bugun fanareti bayan da suka yi canjaras a wasan da ci 5-5.

Jadawalin wasan dab da na kusa da na karshe a gasar Carabao Cup

  • Oxford United da Manchester City
  • Manchester United da Colchester United
  • Aston Villa da Liverpool
  • Everton da Leicester City