Liverpool za ta fice daga gasar Carabao – Klopp

Wasan Liverpool da Arenal kenan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasan Liverpool da Arenal kenan

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce zai yi wuya kungiyarsa ta fito wasan dab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin Carabao, idan hukumar shirya gasar ba ta yi sauyi a ranakun wasannin ba.

Jurgen Klopp ya ce akwai bukatar a yi sauye-sauye a ranakun wasan domin kaucewa karo da wasannin kulob-kulob na gasar cin kofin duniya da hukumar FIFA ta shirya.

Liverpool ta doke Arsenal a bugun fanareti a zagaye na hudu ranar Laraba.

Za a buga wasan zagayen gab da na karshe ranar 16 ga Disamba, amma Liverpool za ta buga wasan ta na gasar cin kofin duniya ranar 18 ga watan Disamba a kasar Qatar.

Sai dai hukumar shirya gasar ta ce suna tattaunawa da Liverpool din don tantance ranar da za a tsayar.

Idan Liverpool ta samu damar fitowa a wasan za ta fafata ne da Aston Villa.

"Idan ba su nemo mafita da wuri ba, da kuma lokacin da ya dace, daga nan zuwa karfe uku na safiyar ranar Kirsimeti, hakka ba za mu yi wasa ba," in ji Klopp.

"Dole ne a yi tunani game da wadannan abubuwan. Idan an riga an fitar da jadawali kungiyoyin da za su fafata ba tare da kulob guda ba, to lallai ne a yi tunani game da batun."

Ma'ana ya kamata a yi wannan ba tare da cin karo da lokutan wasannin wasu kungiyoyi ba.

"Ba za mu yarda matsalar ta shafe mu ba. Mun taka leda a ranar Laraba kuma muna son mu ci nasara.

Idan har ba su samu ranar da ta dace ba, to ba za mu buga wasan zagaye na gaba ba, kuma duk wanda yake abokin karawarmu ne, to zai kara ne da Arsenal. Ba zan iya sauya wannan ba."

Asalin hoton, Robbie Jay Barratt - AMA

Bayanan hoto,

Kungiyar dai za ta buga wasanta da West Ham ranar 20 ga watan Disamba a gasar Premier

Ana gudanar da gasar cin kofin duniya ta kulob-kulob a Disamba kowacce shekara kuma kungiyoyi shida ne da suka fafata a gasar nahiya ke fitowa a gasar.

Lashe gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da Liverpool ta yi a bara ne ya ba ta damar shiga gasar ta FIFA.

Wani mai magana da yawun hukumar ya ce FIFA na fatan ganin Liverpool a Qatar "domin halartar gasar."

Liverpool ta riga ta yanke matakin buga wasanni bakwai a watan Disamba, ciki har da na kusa da na karshe na gasar Carabao.

Kungiyar dai za ta buga wasanta da West Ham ne ranar 20 ga watan Disamba a gasar Premier.