Sterling ya shiga jerin 'yan wasa bakaken fata mafiya tasiri a Birtaniya

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sterling ya bayyana rashin jin dadinsa bayan wasu 'yan kwallo sun yi masa kalaman nuna wariya

Dan wasan gaban Manchester City da kuma Ingila Raheem Sterling ya shiga cikin jerin 'yan wasa bakaken fata mafiya tasiri a Birtaniya.

Jerin sunayen 'yan kwallon bakaken fata da aka saba fitarwa kowacce shekara na mayar da hankali ne kan irin rawar da suke takawa a fannoni da dama da suka hafi harkokin wasanni.

Sterling ya kasance mai adawa da wariyar launin fata a 'yan shekarun nan, duk da cewa ya fuskanci cin zarafin yayin da yake taka wa kulob din a leda da kuma kasarsa.

An sanya sunan Sterling cikin jerin sunayen 'yan kwallo bakaken fata irinsu: Sadio Mane da Danny Rose da Eniola Aluko da kuma Anita Asante.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mane ya koma Liverpool ne a shekarar 2016 daga Southampton

An dai fara fitar da jerin sunayen shahararrun 'yan kwallo bakaken fata a shekarar 2008, yayin da kwararru a harkar tamaula ke zabo 'yan wasan da suke da tasiri.

Ana wallafa sunayen ne bayan wakilan shirya gasar Premier da kwararrun 'yan kwallo da kungiyoyin shirya gasar Lig-Lig da shugabannin shirya gasar Carabao Cup da kuma kungiyoyin yaki da cin zarafin nuna wariyar launin fata sun kada kuri'unsu.

Leon Mann, wanda ya kirkiro da shirin gasar bakaken 'yan kwallo mafiya tasiri, ya ce "Raheem ya yi matukar tasiri bara, haka kuma ya nuna kwazo a ciki da wajen filin wasa.

"Kalmominsa da ayyukansa sun yi matukar tasiri akan yadda za a dakile matsalolin nuna wariyar launin fata da kuma yadda ake kula da bakar fata, ba za a iya yin watsi da su ba.

"Mun yi farin ciki da samun wani sabon abu mai ban mamaki wanda zai taimaka wajen samar da matasa masu kishin bakar fata a nan gaba," in ji Leon Mann.