Premier League: Leicester City ta samu makinta uku

Tawagar Leicesyter City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Leicester ce ta uku a saman teburi

Jamie Vardy da Soyuncu ne suka taimaka wa Leicester City yayin da ta casa Cerystal Palace har gida da ci 0-2.

Jamie Vardy ya zira kwallonsa ta 10 ne a kakar bana ana saura minti biyu a tashi daga wasa bayan sun yi musayar fasin da Garay a cikin yadi na 18 din Palace.

Kafin haka, Caglar Soyuncu ne ya fara jefa kwallo a ragar Palace a minti na 57, inda ya saka wa kwallo kai daga wani bugun kwana da james Maddison ya bugo.

Wannan nasarar ta daga Leicester zuwa mataki na uku a teburi, inda ita kuma Crystal Palace ta gangaro zuwa mataki na tara.

Labarai masu alaka