Guardiola ya zargi 'yan Liverpool da satar hanya

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Guardiola ya ce 'yan wasan Liverpool suna yin sufa

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce 'yan wasan Liverpool na yawan yin gwalangwaso ko satar hanya, abin da ke ba su damar zura kwallo a raga, in ji Guardiola.

Furucin nasa na zuwa ne kwanaki kadan kafin kungiyarsa ta kara da Liverpool din a wasan Premier mako na 12.

Ja-gabar teburi, Liverpool za ta karbi bakuncin mai rike da kambun gasar Man City ranar 10 ga watan Nuwamba.

Sadio Mane ne ya zura kwallo a minti na 94 wanda hakan ya bai wa Liverpool damar doke Aston Villa a wasan da suka fafata ranar Asabar.

"Wani lokacin wasansu satar hanya ne, wani lokacin kuma iyawa ce ke bayar da damar zura kwallo a raga a mintunan karshe," inji Guardiola.

Man City ta kare wasanta da 'yan mintuna kafin Liverpool ta kammala nata, a cewar Guardiola har suka kammala wasa Liverpool din tana 1-1 kuma 'yan mintuna kadan suka rage wasan ya koma 2-1.

"Lokacin da muka yi nasara a wasanmu, Liverpool ba ta yi nasara ba sai gab da za a tashi 'yan wasan suka samu nasarar zura kwallo a raga.

"Abin da ya faru a wasan nasu ba shi ne karo na farko ba, ya faru sau da dama - duk da cewa ana ganin hakan kwarewa ce.

"Don haka sun lashe wasanni da dama a mintunan karshe ne saboda hakan ya zama kamar halayyarsu ce ta musamman.

"Lokacin da muka lashe gasar tare da maki 100 mun yi nasara a wasanni hudu ko biyar a cikin mintinan na karshe."

A kakar wasan da ta gabata ne kocin Cardiff City Neil Warnock ya kwatanta dan wasan Liverpool Mohamed Salah da mai taka leda a gasar Olympic Tom Daley saboda yadda dan wasan yake samar wa kungiyar tasa nasara a wasanni.

Sai dai kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ki amincewa da ikirarin da ake cewa 'yan wasansa na satar hanya a lokacin da suke wasa domin samun nasara.