Premier League: Everton ta rike wa Tottenham wuya

Christian Ericksen Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tottenham ta ci gaba da fuskantar kalubale a kakar Premier ta bana bayan canjaras da ta yi da Everton 1-1 a wasan mako na 11.

Everton ta nuna cewa a gidanta ake wasan domin kuwa ba ta bari an fi ta taka wata rawa ba kuma har zuwa karshensa tana kai kora.

Ta farke kwallon da Dele Alli ya saka mata a raga ne ana saura minti biyar a tashi daga wasan bayan minti 12 da aka kara bayan shafe minti 90 - Cunk Tuson ne ya ci kwallon.

Shi kuwa Dele Alli ya ci tasa kwallon ne tun a minti na 63. Kwallo ce mai kyan gaske inda sai da ya yanke mutum daya sannan ya ratsa bayan Everton kuma ya buga ta gefen hagu na ragar Jordan Pickford.

An kori Son Heung-Min daga wasan bayan ya yi wa Andre Gomes keta, abin da yasa aka fitar da dan wasan a makara, kuma haka Spurs ta kare wasan da mutum 10 a cikin fili tun daga minti na 79.

Sakamakon ya bar tottenham a mataki na 11 da maki 13, yayin da ita kuma Everton ta ci gaba a mataki na 17 kamar yadda ta fara wasan.

Jan kati

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da farko lafarin katin gargadi ya bai wa Son kafin a sauya matakin

Hukumar shirya gasar Premier League ta fitar da wata sanarwa jim kadan bayan tashi daga wasan, inda ta ce:

"An bai wa Son jan kati ne saboda ya jefa rayuwar dan wasa a hadari domin abin ya faru ne ta hanyar abin da ya aikata."

An dai kori Son daga wasan ne a minti na 79 bayan ya yi wa Andre Gomes keta kuma da farko katin gargadi lafarin ya yi niyyar ba shi, amma sai aka sauya hukuncin zuwa katin kora.

Gomes bai iya ci gaba da wasan ba saboda tsananin buguwa da ya yi bayan ya yi karo da Aurier. Shi kansa Aurier bai ji dadin abin da ya faru ba.

Labarai masu alaka