Allegri ka iya zama kocin Bayern Munich

Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty Images

An ba Unai Emery wa'adin wata daya ya kare aikinsa a matsayin kocin Arsenal. (Mirror)

Sai dai Arsenal ta musanta wasu rahotannin da ke cewa tana sha'awar dauko Jose Mourinho. (ESPN)

A gefe guda kuma, daraktan wasanni a Arsenal, Raul Sanllehi, wanda ya shafe shekaru ba su magana da Mourinho, rahotanni sun ce ya ci abincin dare tare da Mourinho. (London Evening Standard)

Tsohon kocin Juventus Max Allegri, da a baya ake rade-radin zai koma Arsenal, ana tunanin shi zai maye gurbin Niko Kovac da Bayern Munich ta kora. (Bild, via Football Italia)

Ana ganin kuma Kocin Leipzig Ralf Rangnick zai karbi aikin na horar da Bayern Munich - Akwai kuma Jose Mourinho da zai iya koma Jamus. (London Evening Standard)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane yana da fatan karbo dan wasan Arsenal William Saliba, mai shekara 20, wanda yanzu haka ke taka leda a St Etienne a matsayin dan wasan aro. (Express)

Tottenham na neman Carles Alena, na Barcelona mai shekara 21, ana tunanin zai koma Ingila a matsayin dan wasan aro a watan Janairu. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan Paris St-Germain naFaransa Kylian Mbappe, mai shekara 20, wata rana zai buga wa Real Madrid, a cewar Vadim Vasilyev, shugabanMonaco tsohon kulub din dan wasan. (Mail)

'Yan wasan Real Madrid biyu da ba su san makomarsu ba Gareth Bale, mai shekara 30, dan kasar Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, ba su fito atisaye ba a karon farko a ranar Lahadi. (Marca)

Labarai masu alaka