Masu nuna wariyar launin fata kun ji kunya – Balotelli

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mario Balotelli ya buga kwallo cikin 'yan kallo sannan ya yi barazanar zai fice daga filin wasan bayan an yi masa kalaman wariyar launin fata a wasan da Verona ta doke kungiyarsa ta Brescia gasar Serie A ta Italiya.

An dai tsayar da wasan cak a lokacin da dan kasar Italiyan, mai shekara 29, ya rike kwallon da hannunsa a minti na 54.

Abokan wasansa na Brescia da kuma mahukuntan wasan sun yi ta lallashinsa kan ya ci gaba da wasan.

Balotelli ya rubuta a shafinsa na Instagram: "Mutanen nan da suka kamanta ni da biri kun ji kunya, kun ji kunya."

Sannan ya saka wani bidiyo na wasu magoya baya suna yi masa ihun wariyar launin fata tare da kwatanta shi da biri.

Ya kara da cewa: "A gaban yaranku da matanku da iyayenku da abokanku da shakikai....kun yi kunya.

"Na gode wa abokan wasana da irin goyon bayan da suka ba ni a ciki da wajen fili da kuma irin sakonnin da na samu daga gare ku.

"Na gode sosai. Kun tabbatar da cewa ku mazaje ne ba irin wadancan ba. #Notoracism."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da kyar aka rarrashi Balotelli ya ci gaba da buga wasan

Bayan an lallashi Balotelli da ya ci gaba da wasan, sai alkalin wasan Maurizio Mariani ya fara aiwatar da matakan yaki da wariya.

An yi sanarwar da ta yi gargadi ga magoya baya cewa idan suka ci gaba da wannan danyen aikin to za a dakatar da wasan baki daya.

Balotelli ya karasa wasan har ma ya ci kwallo daya a minti na 85, sai dai kungiyarsa ba ta iya farke ta biyun ba.

Labarai masu alaka