Tottenham za ta je kotu kan jan katin da aka bai wa Son

Son Hueng-min Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Son ya nuna kaduwa sosai a cikin fili bayan abin ya faru

Ana sa ran Tottenham za ta shigar da kara game da batun jan kan katin da aka bai wa dan wasan gabanta Son Hueng-min a wasan da suka tashi 1-1 da Everton a jiya Lahadi.

An bai wa dan wasan jan kati ne sakamakon ketar da ya yi wa dan wasan Everton Andre Gomes da hakan ya haifar masa da rauni a idon sawunsa,

Ana ganin raunin zai dauki dan wasan tsawon watanni ba tare da ya buga wa Everton wasa ba.

Sai dai Mauricio Pochettino, ya ce bai kamata a kori dan wasan nasa ba.

"Kowa ya gani cewa dan wasan ba da niyya ya yi ketar ba, kuma da ma haka kwallo ta gada. Saboda haka ya kamata mu dauki mataki tunda ba da gangan ya aikata hakan ba kuma ko a fuskarsa za ka gani cewa ya shiga damuwa sosai," inji Pochettino.

Idan har Tottenham din ba ta shigar da kara ba akwai yiwuwar Son ba zai buga wasannin da kungiyarsa za ta fafata da Sheffield United da West Ham da kuma Bournemouth a gasar Premier.

Kocin kungiyar ya kuma ce dan wasan ba shi da wata matsala ta mu'amala da mutane don haka keta ba halinsa ba ne.

Ya ce yanzu haka Son Hueng-min ya shiga damuwa sosai kan abin da ya faru tsakaninsa da Gomez ranar Lahadi.

Labarai masu alaka