Emiliano Sala: FIFA za ta dakatar da Cardiff daga sayen 'yan wasa

Emiliano Sala ya takawa Bordeaux leda kafin ya koma Nantes a 2015 Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Emiliano Sala ya taka wa Bordeaux leda kafin ya koma Nantes a 2015

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta dakatar da kulob din Cardiff City daga saye da musayar 'yan wasa na kakar wasa uku indai ta gaza biyan kungiyar Nantes fan miliyan 15 na dan wasan tsakiya Emiliano Sala ba.

Sala, mai shekara 28, ya mutu ne sakamakon hatsarin jirgin saman da ya rutsa da shi a watan Janairu.

Dan wasan na kan hanyarsa ta zuwa sabon kulob dinsa na Cardiff City daga kungiyar Nantes ta kasar Faransa, lokacin da al'amarin ya faru.

Hukumar FIFA ta ba da cikakkun dalilai game da hukuncin da ta yanke a watan Satumba na umartar Cardiff biyan Yuro miliyan 6.

Sai dai da alama Cardiff za ta daukaka kara kan hukuncin a mako biyu masu zuwa Kotun Sauraron Kararrakin Wasanni.

Kulob din dai ya ce ba shi da alhakin biyan kudin saboda lokacin dan wasan ba ya karkashin kulawarsu a hukumance.

Kwamitin hukumar da ke kula da matsayin 'yan wasan na duniya (PSC) ya yanke hukuncin kan kulob din Cardiff cewa dole ne ya biya kudin da yake cikin yarjejeniyar dan wasan ta sauya sheka.

Rahoton na PSC ya nuna cewa Cardiff na kokarin jinkirta hukuncin FIFA har zuwa lokacin da za a fara shari'ar laifin da ake tuhumarta.

Sun kuma bayar da hujjar cewa kulob din Nantes ne zai 'dauki' alhakin diyya a kan hatsarin jirgin, wanda Willie McKay da dansa Mark suka saya wa masu neman sayen dan wasan tikiti, wadanda kuma kulob din Nantes suke yi wa aiki.

Sai dai McKay ya musanta cewa yana da hannu a zabin jirgin ko matukin jirgin, mai suna Dave Ibbotson, wanda har yanzu ba a gano inda gawarsa take ba.

Kwamitin ya kuma yi watsi da ikirarin Cardiff cewa Sala a lokacin na karkashin Kulob din Nantes

Haka kuma FIFA ta yi watsi da batun Cardiff cewa ba ta kammala sayen dan wasan ba, tana mai cewa hukumar kwallon kafar Wales ta riga ta sanya hannu kan dukkanin abubuwan da suka wajaba, lokacin sa'o'i biyu suka rage jirgin Sala din ya tashi daga Nantes.

Rahoton ya ce: "Sauya shekar dan wasan daga Nantes zuwa Cardiff dole ne a yi la'akari da yadda ya kammala ta tsakanin kungiyoyin biyu, saboda haka dan wasan ya ya rasa ransa ne karkashin Kulob din Cardiff."

PSC ya ce hukuncin ya shafi kudin farko na sauya sheka da dan wasan yayi, da kuma yarjejeniyar da suka kulla wadda zata kare a watan Janairun 202 zuwa 2021.

An dai bai wa Cardiff kwana 45 daga lokacin da Nantes ta ba su cikakkun bayanai na banki don biyan kulob din Faransa fan miliyan 5.3, ban da riba da aka samu tun a watan Janairu.

Labarai masu alaka