Makomar Bale, Sterling, Zaha, Wenger da Mourinho

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid tana shirin bayar da dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 30 hadi da fam miliyan £70 domin karbo Raheem Sterling, mai shekara 24 daga Manchester City. (Sky Sports)

Chelsea na son dan wasan Crystal Palace dan kasar Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 26, da kuma dan wasan RB Leipzigna Jamus Timo Werner mai shekara 23 idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa a Janairu. (Express)

Frank Lampard na Chelseasai ya ware kudi sama da fam miliyan£150 domin cefanen 'yan wasan a Janairu bayan haramtawa kungiyar sayen 'yan wasa. (Telegraph)

Manchester United da Liverpool sun nuna sha'awarsu kan Werner amma RB Leipzigta ce ba ta shirya rabuwa da dan wasan ba a yanzu. (Mirror)

Dan wasan tsakiyarWest Ham na Ingila Declan Rice, mai shekara 20, yana cikin sahun farko da Manchester Unitedke son karbo wa idan an bude kasuwa a Janairu. (Goal)

Chelsea na shiga hamayya da Manchester United kan dan wasan Lyon na Faransa Moussa Dembele, mai shekara 23. (Mail)

Tsohon kocin Chelsea da Manchester United Jose Mourinho ya nuna sha'awar karbar aikin horar 'yan wasan Bayern Munich a cewar tsohon dan wasan Jamus Bastian Schweinsteiger, wanda ya yi aiki karkashin Mourinho a Old Trafford. (Evening Standard)

Tsohon KocinArsenal Arsene Wenger yana cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin Niko Kovac, wanda Bayern Munich ta kora a karshen mako. (Guardian)

Manchester United za ta ci gaba da wasa ba tare da Paul Pogba, na tsawon mako hudu saboda raunin da ya ji a idon kafarsa. (ESPN)

Labarai masu alaka