Hukumar FA ta soke jan katin da aka bai wa Son

Serge Aurier, Andre Gomes da kumaSon Heung-min Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gomez ya ji rauni sosai, inda zai dauki 'yan watanni yana jinya

Hukumar kwallon kafar Ingila (FA) ta soke jan katin da aka bai wa dan wasan gaban Tottenham Son Heung-min bayan ya yi wa dan wasan Everton Andre Gomes keta.

Ketar dai ta janyo wa Gomez ya ji rauni sosai, inda zai dauki 'yan watanni yana jinya.

Alkalin wasa Martin Atkinson da farko ya bai wa Son katin gargadi ne, kafin daga bisani kuma ya sauya zuwa jan kati.

Hakan ta sanya aka kori da dan wasan daga fili ganin cewa ketar ta yi muni, sai dai hukumar ta ce an yanke hukuncin ba bisa ka'ida ba.

Faifan bidiyon da aka nuna ya tabbatar da cewa Gomes ya samu raunin ne sakamakon ketar da Son din ya yi masa, duk da cewa daga bisani ya yi taho mu gama da Serge Aurier.

Yayin jawabi kan matakin Atkinson, hukumar shirya gasar Premier ta ce: "Jan katin da aka bai wa Son na nufin daukar mataki ga barazanar lafiyar dan wasan, wanda ya faru ne sakamakon ketar da ya yi.

Sai dai kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce dan wasan gaban ba da gangan ya ji wa Gomez rauni ba, kuma ya yi amannar cewa ya kamata a yi amfani da na'urar taimakawa alkalin wasa domin janye matakin korar da aka yi masa.

"A bayyane yake cewa ba da gangan ya aikata hakan ba. Abin takaici ne a ce an ba shi jan kati," in ji Pochettino.

Tuni dai aka sallami Gomez daga asibiti bayan an yi masa gyaran karayar da ya samu a kafarsa.

Labarai masu alaka