Jürgen Klopp ya koka game da wasa 2 cikin kwana 2

Jürgen Klopp Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption "Matsalolin a bayyane suke," in ji Klopp

Jürgen Klopp ya ce "bai kamata irin wannan ta ci gaba da faruwa ba" bayan an tabbatar da cewa Liverpoool za ta buga wasa biyu cikin kwana biyu a watan Disamba.

Kungiyar tasa za ta kara da Aston Villa a wasan kwata fayinal na gasar Carabao Cup ranar 17 ga watan Disamba washe gari kuma ta buga sami fayinal a kofin duniya na kulob-kulob wato Club World Cup a kasar Qatar.

"Ya kamata mu nemi mafita," in ji Klopp. "Matsalolin a bayyane suke.

"Duk shekara abin da muke fuskanta kenan. Wasu abin bai dame su ba - wasa biyar cikin kwana uku - bari dai mu ga yadda za ta kasance."

Tun daga 23 ga Nuwamba zuwa 2 ga Janairun 2020 Liverpool za ta fuskanci matsi a wasanninta, inda za ta buga wasa 12 a cikin kwana 37 a gasa hudu: Premier League da Champions League da EFL Cup da Club World Cup.

Sannan kuma akwai wasannin FA Cup wanda har yanzu ba a saka ranar yin su ba - sai a makon farko na 2020 ne za a tsayar da rana.

Da ma a baya Jurgen Klopp ya ce ba za su halarci wasan ba idan har hukumar shirya gasar Carabao Cup din ba ta sauya ranakun wasannin ba.

Liverpool za ta yi wasan gasar kofin duniya na kulob-kulob wato FIFA Club World Cup kwana daya bayan buga wasan na Carabao Cup.

Liverpool dai ta doke Arsenal a bugun fanareti a zagaye na hudu a ranar Laraba.

Klopp ya ce akwai bukatar a yi sauye-sauye ga ranakun wasan domin kauce wa karo da wasannin FIFA Club World Cup.

Hakan na nufin cewa Jurgen Klopp zai shirya tawaga biyu da za su wakilci Liverpool din a wasannin da za ta fafata cikin kasa da sa'a 48.

A baya dai hukumar shirya gasar ta ce suna tattaunawa da Liverpool din domin tantance ranar da za a tsayar.

Wannan shi ne aikin da ke gaban Liverpool a watan Disamba.

Labarai masu alaka