Makomar Xhaka, Wenger, Allegri, Mbappe da Verratti

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce dan wasan Paris St-Germain mai shekara 20 Kylian Mbappe yana da burin zuwa Madrid. (Goal)

Kazalika, Real Madrid ta tattauna da dan wasan tsakiya na Napoli Fabian Ruiz, mai shekara 23, domin karbo dan wasan zuwa Bernabeu a kaka mai zuwa. (ESPN)

Shugabannin Manchester United na son karbo dan wasan Paris St-Germain Marco Verratti, mai shekara 27 da kuma dan wasan baya na Real Madrid Raphael Varane, mai shekara 26. (Manchester Evening News)

Arsenal za ta iya sayar da dan wasan tsakiyarta na Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 27, a watan Janairu bayan tube shi a matsayin kaftin. (Mirror)

Tsohon dan wasan Arsenal Paul Merson ya shawarci kungiyar ta dauko Brendan Rodgers na Leicester City. (Sky Sports)

Tsohon Kocin Italiya Marcello Lippi ya ce Massimiliano Allegri zai fi dacewa ya horar da Manchester United. (Mail)

Shi kuwa Luca Toni cewa ya yi Allegri zai fi dacewa ya horar da Bayern Munich. (Sport1, via Goal)

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce zai iya karbar aikin horar da Bayern Munich. (Bein Sports)

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Chelsea Mason Mount, mai shekara 20, ya yi watsi da kalaman tsohon abokin wasansa Mitchell van Bergen wanda ya ce zai koma Real Madrid ko Barcelona. (Express)

Labarai masu alaka