Wenger zai horar da Bayern, United za ta yi babban cefane a badi

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon mai horar da kulob din Arsenal Arsene Wenger na shirin jan ragamar kulob din Bayern Munich na Jamus har zuwa karshen kakar bana. (Sun)

Mai horar da kulob din Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce watakila ya sayi 'yan wasa biyu kawai a watan Janairu, kasancewar kulob din na da shirin cefano 'yan wasa da yawa a badi. (Evening Standard)

Chelsea za ta saurari tayin kungiyoyi kan dan wasan gabanta Olivier Giroud mai shekara 33 da kuma dan kasar Spaniya Pedro mai shekaru 32, yayin da dan bayanta Marcos Alonso ke fadi tashin ganin ya samu gurbin zama daram a kungiyar. (Telegraph)

Akwai yiwuwar dan wasan tsakiyar Man United Nemanja Matic zai bar kungiyar a watan Janairu. (Manchester Evening News)

Ga alama Chelsea ba za ta sayi dan wasa ba a watan Janairu ko da kuwa an dage mata haramcin sayen 'yan wasan, a cewar mai horar da kulob din, Frank Lampard. (Talksport)

Inter Milan da kuma AC Milan na tattaunawa kan gina sabon filin wasa a kusa da filin wasansu na San Siro da zai lakume fan miliyan 630. Dama kungiyoyin biyu na amfani da filin wasa daya ne. (Mail).

Mai horar da kulob din Barcelona Ernesto Valverde na samun goyon bayan jagorancin kungiyar, duk da cewa akwai damuwa kan yadda kulob din ke taka leda. (ESPN)

Bincike ya nuna cewa sama da kashi 90% na masu goyon bayan kulob din Manchester United ba sa jin dadin yadda ake tafiyar da kulob din. (Telegraph)

Labarai masu alaka