Real Madrid: Rodrygo ne 'sabon' Neymar

Rodrygo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallo uku rigis Rodrygo ya ci a daren jiya Laraba

Dan wasan kasar Brazil Rodrygo ya nuna kansa a idon duniya bayan ya ci kwallo uku rigis a wasan da Real Madrid ta yi ragaraga da Galatasaray da ci 6-0 a gasar Zakarun Turai ta Champions League a daren jiya Laraba.

Rodrygo mai shekara 18, shi ne dan wasa na biyu mafi kankantar shekaru da ya ci kwallo uku rigis a Champions League bayan Raul Gonzalez.

Tuni aka fara kiransa da "sabon Neymar" ganin yadda ya koma kasar Sifaniya da taka-leda daga kungiyar Santos ta Brazil kamar yadda Neymar ya yi - zuwa Barcelona a shekarar 2013.

Matashi Rodrygo mai tsawon kafa 5 kamar Neymar, ba a san shi ba sosai kafin zuwansa Real Madrid a farkon kakar bana.

Tun daga wannan lokaci ne kuma ya jefa kwallo biyar a raga a wasa shidan farko da ya buga wa Real din a dukkanin gasanni.

"Daga sanda na ji an fara rera sunana a Bernabeu na san cewa mafarkina ya zama gaskiya," in ji Rodrygo.

Ya kara da cewa: "Na yi matukar farin ciki, dare ne mai cike da annashuwa amma fa dole na natsu."

Magoya baya a filin wasa na Bernabeu sun fara rera sunan matashin ne tun a minti na hudu da take wasa lokacin da ya bude taron da kwallon farko da kafar hagu bayan Marcelo ya ba shi fasin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shi ne kuma ya rufe taron da kwallo ta shida

Ya ci ta biyu minti uku bayan haka, inda ya saka wa kwallo kai cikin kwarewa bayan Marcelo din ya hango shi cikin taro, abin da ya sa ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo biyu a minti bakwan farko na wasan Champions League.

Ya rufe taron da kwallonsa ta uku bayn ya katse dan bayan Galatasaray da kafar dakma sannan ya ci da kafar hagu, sannan kafiu haka ya taimaka wa Benzema ya ci kwallo ta hudu a minti na 45.

Labarai masu alaka