Pep Guardiola na iya komawa Serie A, Ibrahimović zai koma AC Milan

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Guardiola ya fara jagorancin Man City ne a shekarar 2016

A shirye kocin Manchester City Pep Guardiola yake ya koma horarwa Italiya, idan kwantiraginsa ta kare a Premier a karshen kakar badi, kamar yadda kafar yada labarai ta (Times - subscription required) ta ruwaito.

Dan wasan tsakiya na Arsenal Granit Xhaka zai iya barin kulob din a watan Janairu kuma a shirye Newcastle United take ta sayi matashin mai shekara 27 dan kasar Switzerland, in ji (Times - subscription required).

Barcelona ta nuna sha'awarta ta sayen dan wasan gaba na kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, daga Arsenal, kuma za ta iya yin hakan a watan Janairu, in ji kafar yada labarai ta (El Chiringuito via Mirror)

Dan wasan tsakiya na Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 23, ya shirya tsaf don tattauna wa a mako mai zuwa kan makomarsa a Arsenal, in ji jaridar (Mirror).

A shirye Zlatan Ibrahimović yake don koma wa AC Milan bayan da dan wasan, mai shekara 38, ya bar kungiyar LA Galaxy, in ji (ESPN, via Calciomercato).

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan gaba na kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, zai iya kin karbar tayin koma wa kungiyoyi irinsu Manchester United da Liverpool da Arsenal, ya koma kungiyar RB Leipzig ta Bundesliga daga kungiyarsa ta Red Bull Salzburg a bazarar badi, a cewar (Sky Sports).

Dan wasan Burnley da kuma tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Dwight McNeil, mai shekara 19, ya ce ya fi mayar da hankali a kan kwallonsa maimakon biye wa jita-jitar da ake yadawa ta alakanta shi da kungiyar Manchester United, in ji (Mirror).

Manchester United da Tottenham da Wolves suna gasa kan batun daukar dan wasan gaba na Colombia, James Rodriguez, mai shekara 28 daga Real Madrid a watan Janairu, a cewar (El Desmarque - in Spanish).

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Crystal Palace na sa ido kan nasarar da dan wasan gaba na Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 27, ke samu, wanda ya ci kwallo takwas cikin wasa 15 da ya buga wa Wolfsburg zuwa yanzu a wannan kakar, in ji (Calciomercato - in Italian).

Arsenal da West Ham suna gasa wajen kokarin sayen dan wasan gaba na Austria Martin Hinteregger, mai shekara 27, kan kudi fam miliyan 22 daga Eintracht Frankfurt, in ji (Sun).

Bournemouth da Wolves na sha'awar sayen dan wasan gaba na Ingila, mai shekara 22, Karlan Grant daga Huddersfield a watan Janairu, a cewar (Sun).

Bayern Munich ba za ta dauki Arsene Wenger a matsayin kocinta ba duk kuwa da cewa tsohon kocin Arsenal din ya nuna sha'awar hakan lokacin da ya yi magana da mamallakin kulob din Karl-Heinz Rummenigge a wayar tarho, in ji kafar yada labarai ta (Sky Sports)

Kocin Leicester City Brendan Rodgers ya ce bai kamata tsoron fafatawa ta sa dan wasan gaba na Ingila Jamie Vardy, mai shekara 32, ya ki koma wa Arsenal ba a lokacin da kungiyar ta so daukarsa a shekarar 2016, a cewar jaridar (Telegraph).

Dan wasan baya na Southampton Cedric Soares ya ce zai bar kungiyar a karshen kaka, amma dai matashin dan kasar Portugal, mai shekara 28, na son fara ceto kungiyar tukuna, a cewar (Telegraph).

Wani tsohon dan wasan Manchester United da Juventus ya ce zai iya sanya cacar pizza (wani abinci na Turawa) kan cewa dan wasan tsakiya na Faransa, Paul Pogba, mai shekara 26, zai koma Italian Seria A, in ji(Tuttosport, via Goal).

Labarai masu alaka