Bayern Munich: Ban tattauna da kowa ba - Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wenger ya lashe Premier sau uku a Arsenal cikin shekara 22

Arsene Wenger ya musanta rahotannin da ke cewa zai karbi aikin horar da Bayern Munich.

Sai dai tsohon mai horar da Arsenal din bai nisanta kansa daga aikin ba.

Zakarun Bundesliga, Munich na neman sabon mai horarwa bayan sun kori Niko Kovac a ranar Lahadi biyo bayan kwallo biyar da kungiyar Frankfurt ta dura masu.

Wenger ya lashe kofin Premier sau uku a Arsenal a shekara 22 da ya shafe a kulob din kafin ya ajiye aiki a karshen kakar 2017-2018.

An tambayi dan shekara 70 din lokacin da yake yin sharhi a tashar talabijin ta beIN Sports a ranar Laraba game rade-radin. Sai ya ce:

"Ban taba daina magana da su ba saboda na san jagororin kulob din sama da shekara 30.

"Na kusa koma wa Bayern a shekarun baya. A yanzu dai ban yi magana da kowa ba. Mun dai yi magana a baya amma ban sani ba ko za mu sake yi.

Bayern Munich tana mataki na hudu a teburin Bundesliga, maki hudu tsakaninta da Borussia Mönchengladbach wadda ke saman teburi.

Labarai masu alaka