Ba zan sauya salon taka ledar da nake yi ba - Mane

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto PA Media

Dan wasan Liverpool na gaba, Sadio Mane ya ce ba zai sauya salon yadda yake taka leda ba duk da yadda kocin kulob din, Jürgen Klopp ke goya masa baya wajen kare zarge-zargen da ake yi masa na faduwar da yake yi domin neman fanareti.

An dai ja wa Mane mai shekara 27, kunne a minti na 37 na wasan da suka taka daAston Villa inda aka tashi 2-1, ranar Asabar.

Hakan ne ya sa kocin Manchester City, Pep Guardiola ya fito ya bayyana cewa 'yan wasan Liverpool za su iya iya faduwa domin su samu nasarar.

Mane ya ce "ba zan taba sauya salon taka ledata ba."

"An samu taho-mu-gama a wasanmu da Aston Villa. Kuma watakila ba fanareti ba ne kuma bai bayar ba. Kuma ya ba ni katin gargadi. Zancen gaskiya ba ni da matsala da wannan batu."

Kocin Liverpool din, Jurgen Klopp ya kare Mane inda yake fadin cewa "Sadio ba mai faduwa ba ne. An samu yanayi ne a wasanmu da Aston Villa inda ya yi kacibis da wani har ya fadi, tana iya yiwuwa ba fanareti ba ne amma dai ya yi taho mu-gama. Ba wai ya tsallake kafar wani ba ce ya fadi."

Mane ya yi barkwanci inda ya ce idan ya sake samun wata damar irin wannan to zai sake kwanciya domin neman fanareti.