Premier League: Chelsea ta zama ta biyu a teburi

Tawagar Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan shi ne wasa na shida da Chelsea ta ci a jere a Premier

Tawagar Frank Lampard ta zama ta biyu a saman teburin Premier bayan ta lallasa Crystal Place da ci 2-0 a filin wasa na Stamford Bridge.

Dawowar dan wasa Ngolo Kante ya taimaka wa tsakiyar Chelsea sosai, ganin yadda da ma aka dakatar da Jorginho daga taka-leda.

Wannan shi ne wasa na shida da Chelsea ta ci a jere, abin da ya ba ta damar darewa mataki na biyu a teburi da maki 26 cikin wasa 12.

Tammy Abraham dan kasar Ingila ne ya bude wasan da kwallonsa ta farko, wadda ya ci bayan Willian ya ba shi ita a cikin yadi na 18 din Crystal Palace.

Kazalika, Abraham ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa Chelsea kwallo sama da 10 a Premier- shekarunsa 22.

Sai a minti na 79 ne Christian Pulisic dan kasar Amurka ya jefa ta biyu - Zouma ne ya hango shi a cikin yadi na 18 din Palace, inda shi kuma ya goga mata kai kuma ta gangare zuwa cikin raga ba tare da mai tsaron Guita ya iya yin komai ba.

Kalli yadda aka fafata wasan a nan

Labarai masu alaka