Premier League: Leicester City ta casa Arsenal, ta koma ta biyu

Jamie Vardy da James Maddison Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamie Vardy da James Maddison ne suka yi wa Arsenal biki

Leicester City ta doke Arsenal da ci 0-2 ta kuma koma matsayi na biyu a teburin Premier Ingila.

Wannan ne wasa na biyar a jere da kungiyar ta yi kuma take samun nasara ba tare da la'akari da a gida take ba ko a waje.

Dan wasan gaban kungiyar Jamie Vardy ne ya fara jefa kwallo ta farko a minti na 68 - jimillar kwallo 11 da ya ci kenan a gasar ta bana - kafin daga bisani James Maddison ya kara ta biyu a minti na 75.

Yanzu dai Leicester City ta koma matsayi na biyu a teburin Premier, wanda hakan ke nufin tana saman Manchester City da maki daya kafin ta buga wasanta da Liverpool a gobe Lahadi.

Irin wannan nasarar kungiyar ta rika samu a kakar wasanni ta 2014/2015, wadda ta kai ga ba ta damar lashe gasar a shekarar.

Yanzu dai Leicester za ta je bakunci ne Brighton kafin daga bisani kuma Everton ta ziyarce ta.

Labarai masu alaka