Premier League: Man United ta cinye Brighton, ta koma ta 7

Rashford da Martial Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta lallasa Brighton 3-1 a wasan Premier mako na 12 a filin wasa na Old Trafford.

Sakamkon ya sa Manchester United ta gangaro zuwa mataki na bakwai a teburi da maki 16, maki tara kenan tsakaninta da 'yan hudun farko.

Pereira ne ya fara saka masu masaukin bakin a gaba da kwallon da ya ci a minti na 17 bayan ya buga ta ta daki jikin dan bayan Brighton, abin da ya hana mai tsaron raga Bryan tabuka komai domin hana ta shiga.

Sai kuma D. Propper na Brighton da ya ci gidansu a minti na 19 bayan Harry Maguire da Scott Mc Tominay sun saka masa matsi a bakin ragarsu.

Hakan ya sa Man United ta zama kungiyar da ta fi kowacce amfana da kwallon da abokan wasanta suka ci gida har sau biyar sama da kowacce kungiya a Premier.

Marcus Rashford bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya saka tasa a minti na 66. Anthony Martial ne ya taimaka masa, inda ya ba shi kwallo a cikin yadi na 18, shi kuma ya dada ta har sai da ta bigi tirke kafin ta kwanta.

Wannan nasara za ta saukaka wa mai horarwa Ole Solskjaer ganin irin yadda kungiyar ta yi ta fama da sakamako maras dadin ji a 'yan makonnin nan.

Labarai masu alaka