Wutar daji a Australia ta raba dubbai da muhallansu

The fires have driven thousands of people out of their homes Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wutar daji a wurare fiye da 100 sun raba dubban mutanen kasar da muhallansu

Rahotanni a Australiya na cewa babu alamun wutar dajin da ke cigaba da barna a gabashin kasar na sauki.

Har yanzu 'yan kwana-kwana na bakin kokarin su wurin ganin sun dakile wutar a jihohin South Wales da Queensland.

Hukumomi a jihar South Wales sun yi gargadin cewa babu alamun al'amura za su canza.

Haka ma ba su yi alkawarin kubutar da dukkan mutanen da ibtila'in wutar dajin zai shafa ba.

Wutar dajin ta kashe mutane tare da kona daruruwan gidaje a gabashin kasar ta Ausralia.

Labarai masu alaka