Yadda za ka mallaki gida cikin sauki a Najeriya

Rashin muhalli babbar matsala ce a Najeriya

Batun samar da muhalli ya zama wani muhimmin al'amari, musamman a kasashe masu tasowa kamar Najeriya.

Kididdiga ta nuna cewa ana karancin gida a Najeriya da yawansu ya kai kimanin miliyan 22.

"Kashi 80 cikin 100 na 'yan Najeriya ba su iya gina gida ko kuma su fitar da kudi su saya." In ji shugaban bankin bayar da lamunin gina gidaje na Najeriya Arc Ahmed Dangiwa.

Haka nan matsalar na kara munana da karancin gida 900,000 a kowace shekara.

A kan haka ne Najeriya ta kafa wani banki mai suna Federal Mortgage Bank, wanda ke bayar da lamunin gina gidaje ga al'umma.

Ya tsarin yake?

A wata hira da BBC, Architect Ahmed Dangiwa, ya ce bankin kan bayar da bashi ne domin gina gida ko kuma sayen gida, inda za a rinka cirewa daga albashin ma'aikaci a tsawon shekara 30.

Ya ce a karkashin tsarin, akan cire kashi 1 cikin 40 na albashin ma'aikaci domin sanyawa a cikin asusun gina gidaje.

"Matukar ka fara ajiye irin wannan kudade a asusun tsarin gina gidaje na kasa (National Housing Scheme), to bankin bayar da lamunin gidaje zai iya ba ka bashi daga Naira miliyan 1 zuwa miliyan 15 domin ka gina ko kuma ka sayi gida."

Ka'idojin bayar da bashin mallakar gida:

  • Ya kasance ana ajiya karkashin shirin samar da gidaje na gwamnatin tarayya.
  • Idan za a sayi gida ne, mutum zai nemo gidan da yake so ya siya.
  • Idan gida ne, mutum ya kasance ya mallaki filin da zai gina.
  • Za a yi rajista da kananan bankunan bayar da rancen gina gidaje (Primary Mortgage Bank).
  • Za a biya kashi 10 cikin dari na adadin farashin gida, idan kudinsa ya zarta Naira miliyan 5.

Labarai masu alaka