Premier League: Liverpool ta lallasa City a Anfield

'Yan wasan tawagar Liverpool Hakkin mallakar hoto @LFC
Image caption Tazarar maki takwas Liverpool ta bayar a saman teburi

Liverpool ta gwada wa Man City kwanji tare da tura ta matsayi na hudu a teburin Premier daga matsayi na biyu da take a baya.

Maki 8 ne tsakanin Liverpool da kuma kungiyoyin Leicester City da Chelsea wadanda da ke a matsayi na biyu.

Dan wasan tsakiya Fabinho ne ya fara jefa kwallo a minti na 6 da fara wasan, kafin daga baya Mohammed Salah ya ci tasa a minti na 13.

Hakkin mallakar hoto @LFC

Sadio Mane ne ya kara kwallo ta uku a minti na 51, wadda kuma ita ce kwallo ta 18 da ya ci a wasa 17 da ya buga a filin wasa na Anfield.

Hakkin mallakar hoto @LFC

Bernardo Silva ne ya farke kwallo daya da City ta iya jefawa a makare a watro minti na 78.

Liverpool ce kungiya daya tilo da har yanzu ba a yi nasara a kanta ba a gasar Premier ta bana.

Manchester City ce kawai ta ci Liverpool din a baya a gasar Premier kwana 311 da suka gabata.

Labarai masu alaka