Asenal ta goyi bayan Emery amma ta ce ya kara kaimi

Unai Emery Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Unai Emery

Unai Emery ya samu goyon baya daga mahukuntan Arsenal, sai dai an gargade shi kan ya yi gyara sosai dangane da yadda kungiyar ke gaza tabukawa.

Kocin Arsenal, Emery na fuskantar matsin lamba sakamakon rashin katabus din da kungiyar ke yi.

Nasara biyu kacal Arsenal ta samu a wasannin goman da tayi a gasar Premier.

Sai dai shugaban sashen lura da al'amuran tamaula na kungiyar, Raul Sanllehi da kuma Manajan Daraktanta Vinai Venkatesham sun ce babu wani shirin sauya kocin kungiyar da suke yi a halin yanzu.

"Muna da yakinin cewa Unai shi ne ya dace ya horas da 'yan wasanmu," lokacin da suke shaida wa ma'aikatan kungiyar yayin taro.

"Kamar yadda kowa ba ya jin dadin rashin katabus din kungiyar, mu ma haka muke ji, musamman a kakar bana."

"Ba ma jin dadin halin da magoya bayan suke ciki, Unai, 'Yan wasanmu da kuma ma'aikatanmu, kasancewar suna cikin wani yanayi da ba muyi tsammanin za su shiga ba. Ya kamata a bunkasa abubuwa domin cimma abin da muka sanya a gaba a kakar bana da ma sauran wasanni da ke gabanmu.

"Dukkanin mu muna aiki kan yadda za mu lalubo bakin zaren, kuma muna da kwarin gwiwar cewa komai zai daidaita.

"Arsenal dai ta ce tana fatan za ta samu cikakken goyon bayan da zai ba ta karfin gwiwar dakile kalubalen da ke addbarta halin yanzu.

Labarai masu alaka