Euro 2020: Ingila ta cire Sterling daga tawagarta

Raheem Sterling Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Raheem Sterling

Dan wasan gaba Raheem Sterling ya ce "zuciya ta debe ni" bayan da aka fitar da shi daga jerin tawagar da za su wakilci Ingila a wasan neman shiga gasar Euro 2020.

Ingila dai za ta kara da Montenegro ranar Alhamis, sai dai fadan da ya wakana tsakanin Sterling da Joe Gomez ya sanya aka cire shi.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce an cire Sterling daga tawagar ne sakamakon abin da ke faruwa a kungiyarsa ta daban.

Dan wasan Manchester City, mai shekara 24, daga bisani ne ya sanya shafinsa na sada zumunta cewa komai ya dai daita tsakanin sa da Joe Gomez bayan an samu rashin fahimtar juna a tsakanin su.

"Komai ya dai daita tsakani na da Gomez bayan mun tattauna," inji Sterling ta hannun shafinsa na Instgram.

"Muna irin wasan da ko yaushe sai ka jajirce sosai za ka iya kai zuciyarka nesa, kuma ni mutum ne da nake da saurin fushi.

Sterling ya kara da cewa "Bari mu mayar da hankali kan wasanmu na ranar Alhamis."

sai dai kocin Ingila, Gareth Southgate ya ce: "Abin takaici ne abin da ya faru.

"Daya daga cikin manyan kalubale da muke fuskanta shi ne matsalar hamayyar kungiyoyin waje a tsakanin 'yan wasanmu na gida," inji Gareth Southgate.

Ya ce: "Mun dauki matakin ne ba don la'akari da Raheem ba a wasan da zasu kara da Montenegro ranar Alhamis. abinda na ke ji shi ne fuskantar kalubalen d zai kawo mana cikas.